Beljium Ta Ce Zata Amince Da Samuwar Falasdinu A Cikin Wannan Nan

Gwamnatin kasar Belgium ta bada sanarwan cewa zata bayyana amincewarta da samuwar kasar Palasdinu mai cikekken yenci, a babban taron MDD a cikin wannan watan

Gwamnatin kasar Belgium ta bada sanarwan cewa zata bayyana amincewarta da samuwar kasar Palasdinu mai cikekken yenci, a babban taron MDD a cikin wannan watan a birnin NewsYork.

Shafin yanar gizo na labarai Arab News ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Belgium Maxime Prevot yana fadar haka a shafinsa na X a yau Talata. Ya kuma kara da cewa ya zuwa yanzu dai sun rika sun dauki matakan kakabawa HKI wasu takunkuman tattalin arziki saboda kissan kare dangin da takewa al-ummar Falasdinu a gaza..

A cikin watan Yulin da ya gabata shugaban kasar faransa Emmanuel Macron ya bayyana cewa kasarta zata amince da kasar Falasdinu mai zaman kanta, kafada da kafada da HKI. Bayan haka ne wasu kasashen turai da wasu kasashen duniya suka bi sawunta, inda suka kuduri anniyar amincewa da samar da kasar Falasdi a taron na MDD, wanda za’a gudanar tsakanin 9-23 ga watan satumban da muke ciki.

Yakin da HKI ta fara a gaza, a shekara ta 2023 ya kashe dubban falasdiwa sannan yunwa ta kashe daruruwa saboda hana shigowar a binci zuwa Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted