Sakamakon farko na zaben shugaban kasa da babbar hukumar zaben kasar Belarus ta fitar da jijjifin safiyar yau Litinin ya nuna cewa, Alexander Lukashenko ne ya lashe zaben, inda ya samu kashi 86.82 cikin dari na adadin kuri’un da aka kada.
A bisa dokar kasar ta Belarus dai, ana ayyana duk dan takarar shugaban kasa da ya samu fiye da kashi 50 cikin dari na kuri’un da aka kada a matsayin wanda ya yi nasara
Hakan na nufinb Mista Lukashenko zai jagoranci kasar a wani wa’adi na mulki na bakwai na shekaru biyar.
Hukumar zaben ta sanar da fitowar kashi 81.5% na ‘yan kasar miliyan 6.9 da suka fito rumfunan zabe.