Beirut: HKI Ta Kai Hare-hare A Unguwar Dhahiya Dake Birnin Beirut

Rahotannin daga kasar Lebanon sun ce jiragen HKI sun kai hare-hare sau 17 a cikin unguwar Dhahiya a birnin Beirut. Kafafen watsa labarun HKI sun

Rahotannin daga kasar Lebanon sun ce jiragen HKI sun kai hare-hare sau 17 a cikin unguwar Dhahiya a birnin Beirut.

Kafafen watsa labarun HKI sun ce; harin shi ne mafi girma da HKI ta kai a Lebanon tun bayan tsayar da yaki, kuma tuni sojojin na HKI sun kafa na’urorin kakkabo makamai a arewacin Falasdinu dake karkashin mamaya saboda harin da za a iya kai ma ta daga Lebanon.

Kananan jiragen yaki marasa matuki masu yawa sun rika yin shawagi kasa-kasa a saman birnin Beirut, tare da yin kira ga mazauna yankin da su fice daga gidajensu.

HKI ta riya cewa, wurin da ta kai wa harin, masana’anta ce ta kera jiragen sama marasa matuki, lamarin da majiyar Lebanon ta karyata.

Tashar talabijin ta 12 ta watsa labarin dake cewa; Sojojin Isra’ila suna cikin Shirin yiyuwar a mayar da martani daga Lebanon saboda harin da su ka kai wa Beirut.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments