Batun Fara Kai Wa Isra’ila Hari A Cikin Syria, Lokaci Kadai Yake Jira

Jaridar “Yediot Ahronot” ta HKI ta buga wani rahoto da yake nuni da cewa, da akwai tsoro da razani a tsakanin Isra’ila cewa, za su

Jaridar “Yediot Ahronot” ta HKI ta buga wani rahoto da yake nuni da cewa, da akwai tsoro da razani a tsakanin Isra’ila cewa, za su iya fuskantar hari a cikin Syria, musamman daga yankin tuddan Gulan da suke mamaye da shi.

Jaridar ta kuma ce ko kadan babu wani amfani akan yadda sjojin na ‘yan mamaya suke yin kutse a cikin Syria.

Rahoton ya kuma ce, jami’ian leken asiri sun fara lura da kai da komowar wasu mutane da suke karatar wuraren da sojojin mamayar su ka ja tunga,dake nuni da alamar suna son kai musu hari.

Jaridar ta nakalto dan dahotonta mai yi ma ta sharhi akan harkokin siyasa Yoav Zitun, wanda shi kuma ya ambato wani jami’in soja dake can yankin yana cewa: Batun fara kai mana hari da makami mai linzami, lokaci kadai yake jira, wanda kuma zai iya kai wa ga kashe wasu sojoji.”

Haka nan ya kara da cewa; Komai zai iya sauyawa zuwa yanayi mafi muni.”

Jami’in sojan mamayar ya kuma yi ishara da yadda suke fuskantar wahala a zamansu a cikin yankunan da su ka mamaye a cikin Syria din.   “ Kuma yadda muke cikin kasar da yadda a kullum tankokinmu na yaki suke kai da komawa a cikin Syria, za su iya jawo hankalin masu dauke da makamai su kawo mana farmaki.”

 Har ila yau wannan jaridar ta bayyana cewa, an shiga wani yanayi sau biyu da sojojin mamayar Isra’ila din su ka bude wuta akan mutanen Syria da suke yin zanga-zangar kin amincewa da mamaye kasarsu. Jaridar ta kuma yi gargadin cewa wannan ba zai zama na karshe ba, wato anan gaba za a iya samun wasu su fito yin zanga-zangar ta nuna kin amincewa da sojojin mamaya a cikin kasarsu.

Sojojin Isra’ilan, kamar yadda jaridar ta “Yediot Ahronot” ta ambata sun fara jin suna fuskantar barazana a zamansu a cikin Syria.

A halin yanzu sojojin mamayar Isra’ilan suna tattara  makaman da suke a yankin tuddan Gulan, duk da cewa tsofaffin makamai ne.

Daga cikin makaman da sojojin suke tattarawa da akwai tankokin yaki kirar tarayyar Sovert, da kuma makamai masu linzami da makaman da ke fasa motoci masu sulke da kuma albarusai. Dukkaninsu mallakin sojojin gwamnatin Syria ne da su ka bari.

A fili yake cewa, ko ba dade, ko ba jima sojojin mamayar Isra’ila ba za su cigaba da zama a cikin kasar Syria ba tare da sun fuskanci ‘yan gwgawarmaya ba. Idan ba daga wasu tsofaffin sojojin kasar da su ka rayu da akidar daukar Isra’ila abokiyar gaba fiye da rabin karni ba, to kuma daga samarin kasar da ba za su iya jurewa kallon Isra’ilan tana cigaba da mamaye kasarsu ba.

Illa iya ka lokaci shi ne zai ayyana yaushe hakan za ta faru.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments