Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismael Baqaei ya bayyana cewa Amurka ce Babbar barazana ga zaman lafiya da tsaro a duniya, saboda ganin abinda take yi a halin yanzu a kasar Venezuela da kuma wasu kasashen Afirka.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalyo kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar yana fadar haka a yau litinin a taro da ‘yan jirisa da ya saba a ko wace Litinin.
Baqaei ya kara da cewa a ci gaba da goyon bayan da Washington take bawa HKI ta rufe sararin samaniyar kasar Venezuela, don goyon bayan Falasdinawa, mutanen Siriya da Lebanon da take yi. Wanda kuma ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Dnagne da dangantakar Iran da Saudiya kuma Baqaei ya cewa ziyarar da mataimakin ministan harkokin wajen kasar Saudiya ya kawo nan Tehran, ci gaba ne kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu. Yace abubuwan da Iran da Saudiya suka tattauna a wannan karon sun hada da dangantakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu da kuma al-amura da suka shafi Falasdinu Lebanon da Siriya. Ya ce barazanar da Amurka takewa kasashen Laten Amurka wadanda suka hada da Venezuela, Cuba, Nicaragua Brazil da Mexico duk sun sabawa dokokin kasa da kasa, sannan suna barazana ga zaman lafiya a yankin da kuma duniya gaba daya