Baka’i: Za Mu Mayar Da Martani Akan Wasikar Trump Bayan Yin Nazari

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya ce; Abinda ake watsawa a matsayin wasikar shugaban kasar Amurka shaci-fadi ne, domin har

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Isma’ila Baka’i ya ce; Abinda ake watsawa a matsayin wasikar shugaban kasar Amurka shaci-fadi ne, domin har yanzu, mu ba mu watsa abinda ta kunsa ba.”

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Da akwai banbanci a tsakanin yadda Donald Trump yake Magana a fili da kuma abinda wasikar tasa ta kunsa.

Dr. Baka’i ya kuma kara da cewa; Bayan yin nazarin wasikar da abinda ta kunsa za mu bayar da jawabi.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya kore cewa ziyarar da ministan ma’aikatar tasu Abbas Arakci ya kai zuwa kasar Oman yana da alaka da bayar da jawabin wannan wasikar ta shugaban kasar Amurka.

Da yake mayar da jawabi akan harin da Amurka ta kai wa kasar Yemen, Dr. Baka’i ya ce abin takaici wannan ba shi ne karon farko da Amurkan ta kai wa Yemen hari ba, wanda shakka babu laifi ne kuma abin ayi Allawadai da shi ne.

Dr. Baka’i, ya  kuma yi kira ga kungiyoyin kasa da kasa da kuma kasashen musulmi da kungiyar kasashen ta musulmi da su dauki matakin gaggawa akan abinda yake faruwa.

Dangane da barazanar kai wa Iran hari, kakakin ma’aikatar harkokin wajen na Iran ya ce; Duk wani wuce gona da iri akan Iran zai fuskanci mayar da martani mai tsanani ba tare da taraddudi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments