Kakakin ma’aikatar harkokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran, ya ce; A can baya lokaci mai tsawo, mun rika tuntunbar kungiyoyin adawa na Syria, muna bayyana cewa mun shiga cikin Syria ne bisa gayyatar da gwamnati ta yi mana domin hana hana kungiyar ISIS, yin tasiri, haka nan kuma hana yaduwar ta’addanci daga Syria zuwa cikin kasashen yankin.
Baka’i ya kuma ce; Yana da matukar muhimmanci kar Syria ta zama tungar da ‘yan ta’adda za su yi kyankyawa da zai haddasa rashin tsaro a cikin wasu kasashen yankin.
Dr. Isma’il Baka’i, ya kuma ce, maganganun da ake yi na batunci ga Iran a wannan lokacin ba sababbi ba ne,kuma kokarin da kungiyoyi irin wadannan suke yi domin rusa alaka a tsakanin kasashe ba bakon abu ba ne.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ta Iran wanda ya gabatar da taron manema labaru na mako-mako da yake yi, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar ranar haihuwar Fatimatuz-Zahra (a.s) da kuma taya murnar zagayowar ranar haihuwar annabi Isa ( a.s).