Kungiyar BHRA: Dole Ne A Kawo Karshen Samuwar Sansanonin Sojin Amurka A Bahrain
Babbar kungiya mai fafutukar kare hakkin bil adama a kasar Bahrain ta Bahrain Human Rights Association ta fitar da wani bayani da ke yin kira ga mahukuntan kasar, da su gaggauta daukar matakin kawo karshen samuwar sansanonin sojin Amurka a cikin kasarsu.
Babban sakataren kungiyar Baqir Darwishi ne ya fitar da sanarwar, wadda ta bayyana kasantuwar sansanonin sojin Amurka a kasar a matsayin daga cikin ummul haba’isin matsalolin da yankin gabas ta tsakiya yake a halin yanzu.
Baya ga haka kuma kungiyar ta yi kira da kakkausar murya ga hukumomin Bahrain da su hana sojojin Amurka yin amfani da sansanoni ko sararin samaniyar Bahrain wajen kaiwa wata kasa hari a cikin yankin gabas ta tsakiya.
Kungiyar Karen hakkin bil adama ta Bahrain ta bayyana abin da yake faruwa a halin yanzu a yankin da cewa cewa tsararren shiri ne da ke nufin dagula dukkanin harkokin tsaro a yankin, domin tabbatar da manufofin siyasar kasashen yamma.