Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, kasar Iran ba zata taba zama don tattaunawa da kasar Amurka ba a dai-dai lokacin take kara takurawa kasar da takunkuman tattalin arziki ba.
Tashar talabijin ta Presstva nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka bikin ciki shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin musulunci a kasar a yau litinin, a birnin Hamedan.
Imam Khumaini (q) ne ya jagoranci kasar zuwa ga nasara a shekara 1979, Juyin juya halin da ya kawo karshen Sarautar Muhammad Reza sha Pahlavi.
Ministan ya kara da cewa Jagoran juyin juya halin musulunci ya rika ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Iran kan wannan batun, sannan abinda ya fada shi ne duk wani mai hankali zai koma gareshi.
Ministan ya kara da cewa, gwamnatocin Amurka ba abinda amincewa bane, kuma an jarrabesu an gani, a baya an tattauna da su, basu cika alkawalinsu, kuma ko a yanzun aka shiga wata sabuwar tattaunawa da su, ba bu tabbacin za su yi aiki da abinda aka cimma tsakanin bangarorin biyu ba.
Aragchi ya kammala da cewa. mai hankali ba zai taba amincewa da gwamnatin Amurka ba. Banda haka mutanen Iran sun yi juyinjuya halin musulunci ne don yanke hannun kasashen ketare daga al-amuran kasar. Don haka a halin yanzu ma ba zamu amince da wata kasa ta tilasta mana bin ra’ayinta ba.