Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan.
Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma.
Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba su samu damar sake ganin watan ba. Ga duk wadanda suka samu ganin wannan lokaci mai tsarki cikin halin gudun hijira da tashin hankali, ina so in bayyana sakon tausayawa a gare su.
Ina goyon baya ga duk wadanda ke cikin halin tsanani da wahala, tun daga Gaza da sauran yankuna, zuwa Sudan, Sahel da sauran su. Kuma ina mai ba da hadin kai da masu gudanar da Azumin watan Ramadan da yin kira ga zaman lafiya da mutunta juna. A duk watan Ramadan, na kan kai ziyarar hadin kai tare da yin Azumi tare da al’ummar Musulmi a fadin duniya.
Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci.
A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga kowa.