Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi, za su fuskanci martani mai tsanani
Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) Manjo Janar Mohammad Pakpour ya jaddada cewa: Duk wani kuskuren da makiya za su yi a mashigar tekun Farisa, da mashigar Hormuz da tsibirin Iran, za su fuskanci hukunci mai tsauri, nan take, murkushewa, da kuma nadama.
A cikin sakon taya murnar zagayowar ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Manjo Janar Pakpour ya bayyana cewa: “A jajibirin ranar sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, yana mika sakon taya murna ga babban matsayi na kwamandoji da mayakan da suka yi shahada a lokacin tsaro mai alfarma ta shekara (1980-1988), musamman jaruman dawwama a ranar 16 ga watan Maris ta shekara (1980-1988) a Tekun Fasha da suka hada da -Shahidai Nader Mahdavi, Bijan Kurd, Nasrallah Shafi’i, Gholam Hossein Tavasoli, Mehdi Mohammadiha, Khodadad Absalan, da Majid Mubaraki—waɗanda a cikin yaƙin jarumtaka, suka wargaza girman kan duniya kuma suka mayar da Tekun Fasha tamkar makabarta ga ’yan ta’adda.
Ya kara da cewa: Wannan babbar rana wata alama ce ta tabbatacciyar imani, da gwagwarmayar kaifin basira, da kuma jaddada karfin jarumai masu kishi na sojojin ruwa masu karfi na dakarun kare juyin juya halin Musulunci, wadanda ta hanyar bin umarnin babban kwamandan sojojin kasar (Allah ya kara masa yarda), suka kasance ma’abuta tutar tabbatar da tsaro na dindindin a yankin tekun Farisa, da mashigar Hormuz da mashigar tekun take kewaye da Jamhuriyar Musulunci ta Iran.