Ministan Harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya je kasar Rasha a safiyar yau Alhamis don isar da sakon jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei zuwa shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan sakon na zuwa ne rana guda da amincewar majalisar dojojin kasar Rasha ta dangantaka ta musamman tsakanin kasashen biyu, mai tsawon shekaru 20.
Har’ila yau da kuma kwanaki biyu kafin a gudanar da tattaunawa na biyu tsakanin Iran da Amurka dangane da shirin ta na makamashin Nukliya a birnin Roma na kasar Italiya.
Masana dai sun bayyana cewa kasashen Rasha da Iran suna kara dankon zumunci a tsakaninsu ne a dai-dai lokacinda al-amura da dama suke sauyawa a yankin Asiya da kuma duniya.
Har’ila yau a jiya Larabace ministan ya gana da shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya Raafael Grossi dangane da shirin makamashin nukliya na kasar Iran
A ranar Asabar mai zuwa ne za’a gudanar da tattaunawa karo na biyu tsakanin Iran da Amurka.