Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewa babu abin da ya fi mahimmanci kamar hadin kai ga al’ummar musulmi.
Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana hakan ne lokacin da yake karbar bakuncin masu shirya aikin hajji na iran.
A jawabin da ya gabatar, Ayatullah Khamenei ya yi tsokaci kan aikin Hajji da ake gudanarwa a kowace shekara, wanda ke hada al’ummar musulmi daga sassa daban-daban na duniya ba tare da la’akari da asali, launi, ko al’ada ba.
Jagoran ya ci gaba da cewa: Idan da al’ummar musulmi za su kasance da hadin kai, da matsalolin Falastinu da Gaza ba za su wanzu ba, kuma Yemen ba za ta kasance cikin irin wannan matsin lamba ba.
Ya kara da cewa, ya zama wajibi kasashen musulmi su hada kai, su kuma dakile wahalhalun da suke faruwa a zirin Gaza da Yemen.