A jiya Lahadi ne masu tafiyar da ayarin jiragen ruwan dake son keta killace Gaza ” Sumud” su ka sanar da cewa, tsakaninsu da yankin Gaza bai wuce kilo mita 825 Ba.
Ayarin jiragen ruwan dai yana kunshe da kananan jiragen da sun kai 50, sun fuskanci hare-hare da jiragen sama marasa matuki na HKI da hakan ya haddasa yankewar hanyoyin sadarwa,ba tare da an sami asarar rayuka ba.
Mutanen da suke cikin jiragen ruwan sun hada masu fafutuka da su ka fito daga kasashe 45 na duniya. Daga kasar Malysia kadai da akwai mutane 500 sai Faransawa 54 da kuma ‘yan kasar Belgium 15 daga ciki har da ‘yan gwagwarmayar kare muhalli Greta Thunberg.
Wani daga cikin masu fafutuka dake cikin daya daga jiragen ya watsa wani faifen bidiyo da yake nuna wani karamin jirgin sama maras matuki da yake shawagi a samansu.
Kasashen Italiya da Spain sun sanar da aikewa da jiragen ruwa na yaki domin yi wa jiragen da suke kan hanyar zuwa Gaza rakiya. Daukar wannan matakin na kasashe biyu na turai, ya biyo bayan harin da HKI ta kai wa jiragen ruwan ne.
A karshen watan Ogusta ne dai ayarin jiragen ruwan ya tashi daga tashar ruwa ta Barcelona dake kasar Spain, suna dauke da kayan agaji da su ka hada magunguna.
Wannan ne karon farko da ayarin jiragen ruwa masu yawa su ka kama hanyar zuwa Gaza domin kawo karshen killace yankin da HKI ta yi tun 2006.