AU ta yi Allah-wadai da tsoma bakin kasashen waje a harkokin tsaron Afirka

Hukumar Kula da Harkokin Tarayyar Afirka ta AU ta yi Allah-wadai da duk wani nau’i na tsoma bakin kasashen waje a sha’anin kasashen Afirka da

Hukumar Kula da Harkokin Tarayyar Afirka ta AU ta yi Allah-wadai da duk wani nau’i na tsoma bakin kasashen waje a sha’anin kasashen Afirka da ke fuskantar matsalar tsaro, musamman ma game da rikicin da ake fama da shi a kasar Sudan.

Da yake zantawa da manema labarai ranar Talatar da ta gabata a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, kwamishinan harkokin siyasa, da zaman lafiya da tsaro na kungiyar ta AU Bankole Adeoye, ya ce dole ne kungiyar ta AU ta jagoranci duk wata tattaunawa ta zaman lafiya a nahiyar, yana mai jaddada muhimmancin amfani da ka’idojin warware rikicin Afirka a bisa tafarkin Afirka.

Adeoye ya kara da cewa, “Mu a matsayinmu na kungiyar Tarayyar Afirka, ba mu yarda wani ya yi katsalandan ko rura wutar rikicin da ke faruwa a sassan nahiyar Afirka ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted