AU Na Tattaunawa Kan Batun Ci Gaban Nahiyar Da Zaman Lafiya

An bude babban taron majalisar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka, watau AU karo na 46, a hedkwatar kungiyar da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda taron ya

An bude babban taron majalisar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka, watau AU karo na 46, a hedkwatar kungiyar da ke Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda taron ya jaddada bukatar gaggauta karfafa kokarin da ake yi na bunkasa ci gaban nahiyar, da kwanciyar hankali.

Taron na kwanaki biyu, wanda ya kunshi ministocin harkokin waje na mambobin kungiyar ta AU, ana gudanar da shi ne a karkashin taken da kungiyar ta AU ta fitar na shekarar 2025 : “Adalci ga ‘yan Afirka ta hanyar biyan diyya.”

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban hukumar kula da harkokin AU, Moussa Faki Mahamat, ya jaddada muhimmancin samar da kokarin hadin gwiwa domin inganta zaman lafiya da tsaro a fadin nahiyar.

Ya kuma bayyana wajibcin gudanar da shugabanci nagari, da bunkasa tattalin arziki da zamantakewar jama’a, da samar da isassun kudade masu dorewa, da sake fasalin hukumomin AU.

 Kazalika, ya jaddada bukatar daukaka matsayi da hadin kan Afirka a fagen harkokin duniya.

Bugu da kari, taron zai yi nazari kan daftarin ajanda da shawarwarin taron da za a yi na shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar ta AU karo na 38, wanda aka shirya gudanarwa a tsakanin ranakun 15 da 16 ga watan Fabrairun nan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments