Asia Times: Manyan Dalilan Rushewar Tarayyar Soveit Sun Fara Bayyana Ga Amurka

Mujallar kasar China ta Asia Times ta yi wani sharhi dangane da halin da Amurka ta shiga a yanzu, wanda a cewar mujallar ya yi
Asia Times: Manyan Dalilan Rushewar Tarayyar Soveit Sun Fara Bayyana Ga Amurka

Mujallar kasar China ta Asia Times ta yi wani sharhi dangane da halin da Amurka ta shiga a yanzu, wanda a cewar mujallar ya yi kama da alamun rushewa da suka fara bayyana ga Tarayyar Soveit kafin rushewarta.

Mujallar ta ce, manyan matsaloli na ckin gidan musamman masu alaka da tattalin arziki da rayuwar jama’a, da rashin gamsuwa da yanayin gudanarwa a fili yake a tsakanin al’ummar Amurka.

Baya ga haka kuma shiga cikin rikice-rikice da yakoki yasa makaman Amurka suna karewa, har ma ana karar da makaman fiye da yadda ake kera su, wanda hakan babbar matasala ce ga karfin sojin kasar.

Idan wanann yanayin da Amurka take ciki a yanzu ya ci gaba, tabbas babu makawa makomarta za ta zama irin ta Tarayyar Soveit, domin kuwa ab yanayi da zai bata damar dorewa a matsayin kasa mai karfin iko da fada a ji a duniya ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted