Gwamnatin kasar Argentina ta sanar da ficewarta daga hukumar lafiya ta duniya WHO.
Mai magana da yawun shugaban kasar Manuel Adorni ya fadawa taron manema labarai cewa, shugaban kasar Javier Milei, ya umarci ministan harkokin wajen kasar Gerardo Werthein, da ya dauki matakin janye Argentina daga hukumar lafiya ta duniya.
Adorni ya ce, ” ‘yan Argentina ba za su kyale wata kungiya ta kasa da kasa ta tsoma baki a harkokin da suka shafi ‘yancin kasarmu ba. “
Ya kara da cewa,”Ya kamata a fayyace cewa Argentina ba ta karbar kudade daga hukumar ta WHO don kula da lafiya, don haka, wannan matakin, kamar yadda wasu ke cewa, a kalla a shafukan sada zumunta, ba ya wakiltar asarar kudade ga kasar, kuma ba ya shafar ingancin ayyuka da hidimomi.”