Mataimakin shugaban kasa na farko a nan kasar Iran Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa JMI, kofarta a bude ga tattaunawa da dukkan kasashen duniya in banda HKI. Ya ce mun tattauna hatta da Amurka amma sai suka farmana da yaki a tsakiyar tattaunawar. Don haka Iran tana tattaunawa da dukkan kasashen duniya, sai dai ba zata amince da bukatun da ba zai yu amince da su ba.
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto mataimakin shugaban kasar yana fadar haka a jiya Jumma’a a lokacinda yake ganawa da masu masana’antu a kasar a nan Tehran, ya kara da cewa gwamnatin Amurka ta bukaci tattaunawa da Iran amma tare da sharadin ta amince da bukatarta kafin a fara tattaunawar, amma Iran ta ki amincewa da hakan.
Amurka ta farwa kasar Iran da yaki a tsakiyar tattaunawa, don tilastawa Iran amincewa da bukatarta a tattaunawan ta daktar da tashe makamashin uranium kwata-kwata a kasar, amma gwamnatin JMI ta fuskanceta har da ta nemi tsagaita budewa juna wuta da kanta bayan yaki na kwanaki 12. Iran ta ki ta mika kai ga bukatunta, aka kawo karshen yakin.