Araqchi: Har Yanzu Iran Tana Cikin Halin Yaki Da Makiya

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran ya bayyana cewa: Har yanzu suna cikin halin yaki ba su da kwanciyar hankali Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran ya bayyana cewa: Har yanzu suna cikin halin yaki ba su da kwanciyar hankali

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Kasar Iran tana cikin mawuyacin hali, kuma yakin ya ci gaba har yanzu.

Araqchi ya bayyana cewa: Suna fuskantar yaki, barazanar soja, da kuma takunkumin tattalin arziki masu yawa a cikin yanayin da ake ciki, ya kara da cewa: Gaskiyar magana ita ce kasar Iran tana cikin mawuyacin hali, kuma yakin ya ci gaba gudana.

Araqchi ya kara da bayyana cewa: Har yanzu ba su kai ga wani yanayi na zaman lafiya ba, kuma har yanzu suna nesa da shi, yana mai cewa: Dole ne a yanke duk wata shawara dangane da yanayin da kasar ke ciki a lokacin yaki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted