Minstan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya mayar da martani da kakkausar murya akan furucin jami’ar diplomasiyya ta tarayyar turai Kaya Jallas na cewa Iran ta dakatar da shirinta na makamashin Nukiliya, yana mai cewa; Jallas ta jahilci abinda dokokin NPT su ka kunsa.
Abbas Arakci ya ce; Idan manufar ganawa da kwamitin hadin gwiwa akan yarjeniyar Nukilar iran shi ne kawo karshen Shirin makamashin Nukiliyar Iran, to kuwa Jallas ta jahilci abinda yake kunshe a cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman Nukiliya.
Ita dai babbar jami’ar harkokin wajen tarayyar turai Jallas ta rubuta sako a shafinta na X cewa; Ya zama wajibi a bude tattaunawa da sauri da Iran akan yadda za ta kawo karshen shirinta na makamashin Nukiliya, kuma ficewa daga yarjejeniyar NPT ba zai zama mai taimakawa ba wajen warware batun da yake da alaka da Shirin makamashin Nukiliyar Iran.
Arakci ya kuma ce ; Wannan yana nufin cewa; rawar da tarayyar turai da kuma Birtaniya za su taka a cikin duk wata tattaunawa a nan gaba, za ta zama maras ma’ana.