Ministan harkokin wajen Iran ya kore abinda wasu kafafen watsa labaru su ka watsa na zantawa a tsakaninsa da manzon Amurka a gabas ta tsakiya Steven Witkoff.
Ministan harkokin wajen na Iran, Abbas Arakci ya fada wa kamfanin dillancin labarun “Tasnim” na Iran cewa; Babu gaskiya a cikin labarun da wasu kafafen watsa labaru su ka watsa.”
Ministan harkokin wajen na Iran ya kuma ce; Da akwai tuntubar juna a tsakanin Tehran da Washington kodai ta kai tsaye ta hanyar wasiku, ko kuma ta hanyar masu shiga Tsakani idan bukatar hakan ta taso.”
Wasu kafafen watsa labarun kasashen turai ne dai su ka watsa labarin dake cewa; Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya gana da manzon musamman na Amurka a gabas ta tsakiya Steven Witkoff.
Sai dai ministan harkokin wajen na Iran ya gabatar da shawarar a kulla wata yarjejeniya ta wucin gadi, wacce za ta share fagen kai wa ga cimma yarjejeniya mai dorewa.
Tattaunawa a tsakanin Iran da Amurka, bayan da Washington ta bai wa HKI umarnin kai wa Iran hari, sannan kuma a karshe ita ma Amurkan ta kai wa cibiyoyin Nukiliyar Iran hare-hare.