Arakci: Cinikayya A Tsakanin Iran Da Masar Za Ta Kara Bunkasa

 Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musuluinci ta Iran wanda ya kai Ziyarar aiki kasar Masar ya bayyana cewa, cinikayya a tsakanin kasashen biyu za ta karu.

 Ministan harkokin wajen Jamhuriyar musuluinci ta Iran wanda ya kai Ziyarar aiki kasar Masar ya bayyana cewa, cinikayya a tsakanin kasashen biyu za ta karu.

Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa da takwaransa na kasar Masar ya ce: “A bisa yarjejeniyar da bangarorin biyu su ka cimmawa za a kara girman kasuwancin da ake tsakanin Iran da Masar.”

Abbas Aragchi ya godewa mai masaukinsa na Masar Badar Abdulatif, saboda tattaunawa mai muhimmanci da su ka yi.”

Bugu da kari Abbas Arakci ya yi wa shugaban kasar Masar godiya saboda ganawa da ya yi da shi, yace: Wannan Shi ne ganawata ta hudu da shugaban da shi daga sheakarar da ta gabata’.

Har ila yau, ministan harkokin wajen na Iran ya yaba ganawar da aka yi a tsakanin shugabannin kasashen Iran da na Masar, a taron kungiyar kasashen musulmi da aka gudanar a bara. Sannan ya kammala da cewa wannan yana nuna irin muhimmancin da kasashen biyu suke daukar juna.

Da yake Magana akan yakin Gaza kuma, ministan harkokin wajen na Iran ya jinjinawa Masar da Qatar saboda kokarin da suke yi na ganin an dakatar da yaki.”

Dangane da tattaunawar Nukiliya tsakanin Iran da Amurka kuma, ministan harkokin wajen na Iran ya ce: Manufar tattaunawar ita ce tabbatar da cewa Iran baa ta nufin kera makamin Nukiliya, kuma akwai yiyuwar a kai ga cimma yarjejeniya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted