Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, duk wata barazana da za a yi wa Iran za ta sa makiya su yi babbar nadama.
A wata hira a tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta yi da shi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, farfagandar da ake yi ta cewa, kai wa kasar Yemen hari share fage ne na yaki da Iran ba sabon abu ba ne, an sha yin irin wannan barazanar a baya.
Abbas Arakci ya kara da cewa; Iran ba za ta taba kyale duk wani mahaluki da zai rika yin Magana da ita da harshe na barazana ba, sannan ya kara da cewa makiya za su yi nadamar wannan barazanar.
Da yake Magana akan cigaba da kai wa Yemen hare-hare da Amurkan take yi, ministan harkokin wajen na Iran ya ce, nasarar da Yemen din take samu ne ya sa hakan take faruwa,kuma a cikin shekaru 10 na hare-haren da ake kai wa Yemen har yanzu an kasa yin galaba akan ta.