Araghchi zai fara ziyarar kwanaki biyu a kasashen Masar da Lebanon

A wani lokaci yau Litini ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai fara ziyarar kwanaki biyu a kasashen Masar da Lebanon. Yayin ziyarar Araghchi

A wani lokaci yau Litini ne ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi zai fara ziyarar kwanaki biyu a kasashen Masar da Lebanon.

Yayin ziyarar Araghchi zai gana da manyan jami’an Masar da na Lebanon domin tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu dama rikicin yankin.

Ziyarar Araghchi a Masar za ta gudana ne bisa gayyatar takwaransa na Masar Badr Abdelatty.

Ana sa ran ministan harkokin wajen na Iran zai gana da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi, da takwaransa Badr Abdelatty, da kuma wasu masu fada a ji a fannin tattalin arzikin Masar.

Da yake karin haske kan manufar ziyarar, mai kula da harkokin Iran a Alkahira ya ce, rikice-rikicen yankin da suka hada da hare-haren wuce gona da iri na Isra’ila a Gaza da kuma rikicin Sudan da Libya, na daga cikin batutuwan da bangarorin zasu musayar ra’ayi .

Dangane da alakar da ke tsakanin Tehran da Alkahira, ya ce ana ci gaba da samun ci gaba, tare da tuntubar juna da tattaunawa mai zurfi tsakanin ministocin harkokin wajen kasashen biyu.

Ya ce yana fatan Iran da Masar za su dauki mataki na karshe don kyautata alakarsu nan gaba kadan. Ban da haka kuma, Iran tana goyon bayan adawar Masar na tilastawa ‘yan Gaza gudun hijira.

A watan Disamba na shekarar 2024, shugaban kasar Iran Massoud Pezechkian ya ziyarci Masar, ziyarar farko da shugaban kasar Iran ya kai kasar Larabawar tun shekara ta 2013.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments