Search
Close this search box.

Araghchi, Ya Tattauna Da Takwaransa Na Jordan Kan Rikicin Falasdinu  

Ministocin harkokin wajen kasashen Jordan da kuma na Iran sun tattauna game da rikicin Falasdinu. A wata zantawa ta wayar tarho da takwaransa na Jordan,

Ministocin harkokin wajen kasashen Jordan da kuma na Iran sun tattauna game da rikicin Falasdinu.

A wata zantawa ta wayar tarho da takwaransa na Jordan, Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana ta’asar da Isra’ila ke yi a matsayin babban abin da ke haifar da kara tabarbarewar al’amura da tashe-tashen hankula a yankin yammacin Asiya.

Kalamman nasa sun zo ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kisan kare dangi a zirin Gaza da yadda take ci gaba da kai munanan hare-hare a yankin yammacin gabar kogin Jordan da aka mamaye, da kuma kai munanan hare-hare a kan kasar Labanon.

A matsayin misali, Mr. Araghchi ya nuna cewa gwamnatin ta kasance babban cikas ga cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da za ta iya kawo karshen yakin da ake yi da Gaza, wanda ya janyo asarar rayukan Falasdinawa sama da 40,600, galibin mata da kananan yara.

Araghchi Ya jaddada bukatar daukar kwararan matakai na kasashen duniya domin kawo karshen kisan kiyashi da kuma isar da agajin jin kai a gabar tekun.

A nasa bangaren jami’in na Jordan ya ce: Wajibi ne a kawo karshen zaman dar dar a zirin Gaza da yammacin gabar kogin Jordan da wuri. »

Jami’ai sun kuma bayyana ci gaba da tuntubar juna tsakanin Tehran da Amman, tare da ganin cewa, shawarwarin sun dace da moriyar kasashen biyu da ma yankin baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments