Araghchi : wurin da za a yi zagaye na gaba na tattaunawa da Amurka zai iya canzawa

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce wurin da za a yi zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin kasar da Amurka zai iya canzawa.

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya ce wurin da za a yi zagaye na gaba na tattaunawa tsakanin kasar da Amurka zai iya canzawa.

Araghchi ya yi wannan furuci ne a wata hira ta musamman da Al Jazeera sashen Larabci bayan ya gabatar da jawabi a matsayin bako na musamman a yayin bude taron Al Jazeera Forum a Doha babban birnin Qatar.

Tawagar Iran da Amurka, karkashin jagorancin Araghchi da manzon musamman na Amurka Steve Witkoff, sun sake fara tattaunawar nukiliya a Muscat babban birnin Oman a ranar Juma’a, watanni takwas bayan yakin Isra’ila da Iran a watan Yunin da ya gabata.

Araghchi ya shaida wa Al Jazeera cewa bayan kimanin sa’o’i shida na tattaunawa, jami’an diflomasiyyar Iran da Amurka sun amince su gudanar da zagaye na biyu na tattaunawa, kodayake ba a sanya ranar da za a yi ba tukuna.

Duk da haka, ya ce, Tehran da Washington sun yi imanin cewa dole ne a gudanar da tattaunawar “nan ba da jimawa ba,” kuma ba a sanar da wurin taron ba tukuna.

An shirya zagaye na farko na tattaunawa kai tsaye tsakanin Iran da Amurka a Istanbul, amma, Iran ta nemi a sauya wurin zuwa Muscat, na kasar Oman, wadda ta shiga tsakani a tattaunawar da ta gabata tsakanin Tehran da Washington.

Araghchi ya kara da cewa akwai yiwuwar yaki da Amurka a koyaushe, yana mai nanata cewa Jamhuriyar Musulunci ta shirya “don zaman lafiya da yaki.”

Ya tabbatar wa kasashen yankin cewa idan Amurka ta kai hari, Iran za ta kai hari ne kawai ga sojojin Amurka da ke yankin, ba ƙasashen da kansu ba.

“Ba za mu kai hari ga kasashen makwabta ba; maimakon haka, za mu kai hari ga sansanonin Amurka da ke cikinsu. Akwai babban bambanci tsakanin su biyun,” in ji Araghchi.

Ya jaddada cewa batutuwan da suka shafi shirin nukiliya na Iran za a iya warware su ne kawai ta hanyar tattaunawa, amma ya yi watsi da duk wani tattaunawa kan makamai masu linzami na kasar, wadanda ya ambata da batu na kariya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted