Araghchi : Trump bai cancanci mai samar da zaman lafiya ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya caccaki Donald Trump kan manufofinsa a yammacin Asiya, yana mai cewa shugaban Amurka ba zai iya da’awar samar da

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya caccaki Donald Trump kan manufofinsa a yammacin Asiya, yana mai cewa shugaban Amurka ba zai iya da’awar samar da zaman lafiya a yankin ba yayin da yake aiwatar da manufofin wuce gona da iri da kuma hada kai da “masu aikata laifukan yaki.”

A cikin wani sako a shafinsa na X, Abbas Araghchi ya ce ikirarin da Trump ya yi a baya-bayan nan na cewa “ya rage makwanni” Iran ta kera makamin nukiliya kafin harin da Amurka da Isra’ila suka kai kan cibiyoyin nukiliyarta ” karya ce.”

“Wannan kawai KARYA ce tsungurungum dinta, kuma ya kamata a sanar da shi cewa babu tabbacin hakan, kamar yadda jami’an leken asirinsa suka tabbatar masa.”

Jami’in diflomasiyyar na Iran ya yi Allah-wadai da matakin da Amurka kan hare-haren da aka kai wa Iran a watannin baya, wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula sama da 1,000 da suka hada da mata da kananan yara.

Araghchi ya ce Trump “na iya zama shugaban zaman lafiya ko kuma shugaban yaki, amma ba zai iya zama duka a lokaci guda ba.”

Ministan na Iran na maida martini ne kan yadda Trump ya bayyana kansa a matsayin mai samar da zaman lafiya da kuma kalamansa na cewa zai samar da zaman lafiya mai dorewa a fadin yankin, tare da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.

Araghchi ya ce Iran tana shirye ga “mutunta duk wani yunkurin na diflomasiyya domin cin moriyar juna,” amma kasar ba za ta amince da barazana ko tilastawa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments