Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a gobe talata mataimakin shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya zai ziyarci kasar, amma ba tare da zuwa cibiyoyin nukliya na kasar ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne ziyarar aiki na farko wanda wani jami’in hukumar ya kawo ziyara Tehran bayan yakin kwanaki 12 wanda HKI ta dorawa JMI.
Gwamnatin JMI dai tana shakkan ma’amatar da hukumar, inda take ganin babu gaskiya a cikin mu’amalarta da ita, da farko saboda tabbacin cewa hukumar tana bawa makiyanta, musamman HKI wasu bayanai wadanda ta karba a wajenta dangane da shirinta na makamashin nukliya, inda HKI ta sami damar kashe masana fasahar nukliyar kasar da dama a cikin shekarun da suka gabata.
Banda haka hukumar ta IAEA ta tara gwamnoninta suka kada kuri’ar rashin amincewa da shirin makamashin nukliya da rana guda sai HKI ta kawowa Iran hari. Wannan ya nuna kamar akwai aiki tare tsakanin hukumar da HKI.
Wannan matsalolin da kuma debe kauna kan cewa hukumar zata yiwa Iran adalaci majalisar dokokin kasar Iran ta fidda doka wacce ta jingine mu’amala da hukumar.
A wannan ziyarar dai bangarorin biyu zasu fidda sabbin hanyoyin mu’amala da hukumar tare da lura da korafe-korafen JMI a ayyukan hukumar a yanzu.