Araghchi: Iran Za Ta Yi Duk Abinda Ya Dace Don Fitar Da Mai

A watan Afrilu ne Amurka ta sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa na Iran.

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa Tehran za ta yi duk mai yiwuwa don fitar da man fetur dinta da kuma karya matakin Amurka kan tashoshin jiragen ruwanta.

Mista Araghchi ya bayyana hakan ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na ILNA, a yayin da ake samun rahotannin cewa Iran na shirin aika jiragen ruwa na man fetur duk da matakan da Amurka ta dauka kan jiragen ruwanta.

“Dole ne a karya dokar,” in ji shi, inda Ya kara da cewa Iran za ta yi duk mai yiwuwa don fitar da man fetur dinta yayin da ake ci gaba da tattaunawa.

A watan Afrilu ne Amurka ta sanya dokar hana zirga-zirgar jiragen ruwa na Iran.

Tehran ta mayar da martani inda ta toshe hanyar jiragen ruwan Amurka da kawayenta ta cikin mashigin teku na Hormuz.

Wannan yanayi ya kawo cikas ga samar da makamashi a duniya, wanda ya haifar da hauhawar farashin mai, musamman a Amurka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted