Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa ta hanyoyin da suka dace.
Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kai tsaye a gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) jiya Alhamis.
Araghchi ya kuma lura cewa a wannan karon, ci gaban ya zo tare da wani yunkuri na diflomasiyya daga Amurkawa, ciki har da wasika da bukatar yin shawarwari.
Ya kuma bayyana cewa manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bayyane take. “Ba za mu shiga tattaunawa kai tsaye karkashin matsin lamba, barazana, ko karin takunkumi.”
A cewar Araghchi, tilas ne a gudanar da shawarwari bisa daidaito da kuma kyakkyawan yanayi.
Ministan harkokin wajen kasar ya kuma bayyana cewa wasikar “mafi yawan barazana ce,” amma kuma akwai damamaki a ciki.
“Mun yi nazari sosai kan dukkan bangarorin wasikar, tare da yin la’akari da kowane daki-daki sosai,” in ji shi.
A farkon watan Maris ne Trump ya bayyana cewa ya rubuta wasika zuwa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.
A karshen watan Fabrairu, Ayatullah Khamenei, a wata ganawa da jami’an sojin sama a Tehran, ya bayyana cewa bai ga amfanin tattaunawa da Amurka saboda ba zata warware matsaloli ba.
Kalaman nasa sun zo ne sa’o’i bayan da gwamnatin ta Trump ta kakaba wa Iran takunkumai da Trump ya bayayana da “mafi girman matsin lamba” kan Iran.