Araghchi : Iran Ba Za Ta Shiga Tattaunawa Da Amurka Bisa Matsin Lamba

Iran ta bayyana cewa ba zata shiga wata tattaunawa da Amurka ba kan shirinta na nukiliya bisa matsin lamba. Ministan harkokin wajen Iran ne Abbas

Iran ta bayyana cewa ba zata shiga wata tattaunawa da Amurka ba kan shirinta na nukiliya bisa matsin lamba.

Ministan harkokin wajen Iran ne Abbas Araghchi ya bayyana hakan, inda yake cewa muddin fadar White House ba ta janye matsin lamba wa kasar ba, babu wata tattaunawa.

“A kan tattaunawar nukiliya, matsayin Iran a bayyane yake: ba za mu yi shawarwari cikin matsin lamba, barazana, da takunkumi ba.”

“Saboda haka,” in ji ministan harkokin wajen Iran, “babu yuwuwar yin shawarwari kai tsaye tsakaninmu da Amurka kan batun nukiliya matukar dai ana ci gaba da yin amfani da mafi girman matsin lamba a yadda take a halin yanzu.”

Misra Araghchi ya bayyana hakan ne a yayin  wani taron manema labarai da takwaransa na Rasha, Sergey Lavrov da ke ziyara a Tehran.

Ministan harkokin wajen kasar ya ce Iran za ta magance batun nukiliyar tare da hadin gwiwa da kawayenta – Rasha da China.

A nasa bangare da yake bayyani game da shirin nukiliyar Iran, Lavrov ya ba da fifiko kan hanyar diflomasiyya.

“Mun yi imanin cewa har yanzu akwai karfin diplomasiyya don warware batun nukiliyar Iran, kuma muna fatan za a iya samun mafita. Ba Iran ce ta haifar da wannan rikicin ba.” Inji shi.

Iran dai ta dade tana fuskantar takunkumin da kasashen yamma suka kakaba mata kan ayyukanta na nukiliya, da batun kare hakkin bil’adama, da dai sauransu, saidai zuwan Donald Trump, ya kara dagula al’amuran inda ya sha alwashin matsin lamba kan kasar ta Iran, domin ta mika wuya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments