Araghchi : Iran a shirye take ta shiga tattaunawa da Turawa bisa mutunta juna

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunawa da kasashen Turai bisa mutunta juna. A wata tattaunawa ta

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran a shirye take ta shiga tattaunawa da kasashen Turai bisa mutunta juna.

A wata tattaunawa ta wayar tarho, Araghchi da Ministan Harkokin Wajen Netherlands Caspar Veldkamp sun tattauna hanyoyin inganta alakar juna da sabbin abubuwa dake faruwa a yankin da na kasa da kasa.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya nanata tsarin kasar na kulla kyakkyawar alaka ta diflomasiyya da kasashen.

Iran da kasashen Turai dai na tattaunawar ba-zata kai a kai tun shekara ta 2021, shekaru uku bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar iran – tare da maido da takunkumin da Washington ta kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

bangarorin kasashen Turai da suka shiga yarjejeniyar nukiliya – Birtaniya, Faransa da Jamus – sun kasa cika alkawarin da suka dauka na dawo da Washington cikin yarjejeniyar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments