Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce duk wani ci gaba da za’a samu a tattaunawa da Amurka ya dogara ne da muhimmancin da Washington ta ba tattaunawar.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, Araghchi ya ce barazana da kuma takunkumin da Amurka ke kakaba wa Iran, ya kara haifar da shakku game da aniyar Washington na neman hanyar diflomasiyya.
“Don ci gaba a kan wannan tafarki dole ne dayan bangaren ya nuna kyakkyawar niyya cewa da gaske ya ke,” in ji shi, kafin ya ce: “Iran, a matsayinta na mamba a yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT), dole ne ta ci moriyar makamashin nukiliya don dalilai na zaman lafiya.”
Ministan na Iran ya kara jaddada cewa, domin cimma daidaito, da kuma dawwamamiyar yarjejeniya, tilas ne dukkan bangarorin su kaurace wa duk wasu bukatu da suka saba wa yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya.
Abbas Araghchi ya kuma yi tsokaci kan gazawar Amurka wajen cika alkawuran da ta dauka karkashin yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015, yana mai jaddada cewa dole ne sauran bangarorin su ba da tabbacin dage takunkumin da aka kakaba iran.
A nasa bangaren babban sakataren MDD ya jaddada muhimmancin ci gaba da tattaunawa har sai an samu sakamako.
Mr. Guterres ya kuma yaba da sabbin hanyoyin da ministan harkokin wajen Iran ya bi wajen bayyana abubuwan da ke faruwa a tattaunawar ta tsakanin Iran da Amurka.