Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, ci gaban taron zaman lafiya na birnin Astana ya ta’allaka ne kan ci gaban da za a samu a kasar Siriya a nan gaba da kuma shawarar da Iran, Rasha da Turkiyya suka yanke.
Araghchi ya gabatar da rahoto ne kan harkokin siyasa da ake gudanarwa kan sabbin abubuwan da suke faruwa a kasar Siriya biyo bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad.
“A cikin wannan taron, na gabatar da rahoto kan ayyukan diflomasiyya da aka gudanar a cikin ‘yan kwanakin da suka gabata, musamman tarukan da aka yi a Doha,” in ji Araghchi.
A ranar Lahadin da ta gabata ce dakarun ‘yan adawar kasar Siriya masu dauke da makamai suka kwace iko da birnin Damascus ba tare da wata turjiya daga sojojin Siriyan ba, bayan da aka fara farmakin na tsawon kwanaki goma da kwace birnin Homs, da kuma Hama a rana ta biyu da ta uku na hare-haren.
Bashar al-Assad ya bar Damascus ne tare da iyalansa, inda gwamnatin Rasha ta ba su mafaka.