Iran, ta sanar da cewa a halin yanzu ba ta da wani shiri na tattaunawa da Amurka.
Da yake sanar da hakan Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya ce a halin yanzu Tehran ba ta da niyyar shiga tattaunawa da Washington, saboda babu wata madogara ta irin wannan tattaunawa.
Ya ce Iran na jiran ta ga irin manufofin da sabuwar gwamnatin Amurka za ta aiwatar kafin ta yanke shawarar kanta.
A wata hira da ya yi da tashar Al-Araby Al-Jadeed, Araghchi ya tattauna batutuwa da dama da suka hada da halin da ake ciki a Siriya, yakin Gaza, tattaunawar nukiliyar Iran da Turai da tattaunawa da Amurka.
Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya ce yana shirin kai ziyara kasar Rasha domin tattaunawa kan al’amuran da ke faruwa a kasar Siriya, yana mai jaddada cewa Iran na shirin yin tsayuwar daka don taimakawa wajen kwantar da hankula a kasar ta Siriya da kuma samar da wata dama ta wani shiri da zai kai ga cimma matsaya ta dindindin.
Ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kullum tana neman tuntubar juna da tattaunawa da Turkiyya, inda ya kara da cewa fadada ayyukan kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Siriya na iya haifar da babbar barazana ga kasashen da ke makwabtaka da Siriya kamar Iraki da Jordan da Turkiyya, da kuma Iran.
Ya kuma jaddada cewa, idan gwamnatin Syria ta bukaci Iran ta tura dakaru zuwa Syria, to Tehran za ta duba wannan batu da idon basira.