Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Iran a shirye take game da dukkanin abin da Amurka ta zaba.
Araghchi ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce ga dukkanin alamu gwamnatin Amurka tana fifita bin Netanyahu ido rufe wajen aiwatar da manufofinsa, ba tare da la’akari da maslahar Amurka da al’ummarta ba.
Ya ce a duk lokacin da ake kokarin raya ruhin diflomasiyya, Netanyahu yana yin dukkanin kokarinsa domin kashe wannan ruhin, kuma Amurka tana binsa a hakan ido rufe.
Ya kara da cewa, Iran a shirye take game da duk abin da Amurka ta zaba, bin hanyoyin na diflomasiyya ko kuma bin Netanyahu wajen ci gaba da haifar da tashe-tashen hankula a yankin, domin kuwa a cewarsa Iran za ta ci gaba da kare kanta da kuma mayar da mummunan martani a kan duk wanda ya yi shishigi a kanta.