Araghchi: Babu Hannun Iran A Harin Makami Mai Linzami A Kan Turkiyya

Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, babu hannun Iran a harin makamai mai linzami da aka kai kan kasar Turkiya.

Araghchi ya bayyana hakan ne a wannan Talata a lokacin zantawarsa da takwarnsa na kasar Turkiya ta wayar tarho, inda ya jaddada cewa, kasarsa tana mutunta kyakkyawar dangantaka da ke tsakaninta da makwabciyarta Turkiya.

A kan haka ya ce ba su da wata masaniya a kan makami mai linzzami da aka harba a kan Turkiya, kuma a shirye suke su hada hannu tare da Turkiya domin gudanar da bincike a kan lamarin.

Ministan Harkokin Wajen Kasar ta Iran ya ci gaba da cewa, tun kafin wannan lokacin sun sanar da cewa, Amurka da Isra’ila suna kai hari a kan wasu kasashe domin tuhumar Iran da yin hakan, wanda kuma a cewarsa Iran ba ta boye hare-harenta wadanda sun takaita ne kawai a kan Isra’ila da Amurka da kuma kaddarorinsu da ke cikin kasashen yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted