Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya isa birnin Kampala babban birnin kasar Uganda don halattan taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar yan ba ruwammu karo 19 .
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran za’a gudanar da taron ne tare da neman ‘shi’arin “zurfafa hadin kai da kuma rabon fahintar juna a duniya’. Ana saran Jami’an dublomasiyya da jakadu daga kasashe duniya 120 ne zasu halarci taron karo na 19 a birnin Kampala.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’ila Baghaei ya bayyana cewa banda tattaunawar wadan nan kasashe a tsakaninsu kan al-amura da dama, a gefen taron kuma kwamitin Falasdinu na kungiyar zai gudanar da taronsa, wanda gwamnatin JMI take cikinsa.
A taron dai ana saran ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi zai gabatar da jawabi kan al-amura da suka shafi kungiyar da kuma tattaunawa da suka saba yi musamman kan al-amuran da suka tattauna a bayan. Banda haka ministan zai tattauna da tokwarorinsa da dama daga sauran kasashen duniya kan al-amuran da suka hadasu da JMI, imji Baghaaei.