Aragchi Ya Ce Hanyar Diblomasiyya Ce Kadai Hanar Warware Matsalar Shirin Nukliyar Iran

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hanyar deblomasiyya ce kadai zata warware matsakar shirin nukliyar kasar iran da kasashen yamma. Kamfanin

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa hanyar deblomasiyya ce kadai zata warware matsakar shirin nukliyar kasar iran da kasashen yamma.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto ministan yana fadar haka a zantawa ta wayar tarho da jami’a mai kula da al-amuran harkokin waje na kungiyar tarayyar Turai Kaja Kallas.

Labarin ya kara da cewa ministan yana ganin matsalolin shirin Nucliya da kuma tsaron kasar ba za’a iya warwaresu ba sai ta wannan hanyar.

JMI ta dauki wannan hanya ce don ita ce kadai wacce zata kai da gamsuwar ko wani bangare a cikin al-amuran da suke sabani a cikinsu. Aragchi ya fadawa Kallas kan cewa da wannan dalilin ne JMI ta dauki hanyar tattaunawa ba kai tsaye ba don warware matsalra ta da Amurka.

Ya ce a shekarun da suka gabata JMI ta sha tattaunawa da kasashen turai Ingila, faransa da Jamus amma sai a zo inda suke tashi baram-baram, don kowa ya tsaya a kan matsayinsa.  Sannan ya kammala da cewa don kaucewa sabani dayan bangaren bai kamata ya gabatar da wani al-amari wand aba zai yu ba.

A nata bangaren Kallas ya bayyana cewa kungiyar kasashen Turai a shirye take ta shiga tattaunawa ta siyasa da JMI sannan a halin yanzu kungiyar tana neman lokacinda ya dace don yin hakan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments