Aragchi: Iran Ba zata Taba Daina Tace Makamashin Uranium A Cikin Gida Ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa shirin makamashin nukliya na kasar Iran kuma na zaman lafiya ya zama abin alfakhari ga

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa shirin makamashin nukliya na kasar Iran kuma na zaman lafiya ya zama abin alfakhari ga mutanen kasar da daukaka. Don haka gwamnati mutanen kasar ba zasu taba yarda a barshi ba.

Ministan ya bayyana haka ne a lokacin da yake hira da tashar talabijin ta CBS news na kasar Amurka dangane da hare-haren da HKI da kuma Amurka suka kaiwa kasar a cikin watan yuni da ya gabata. Hare-haren  da aka kaiwa kasar a dai-dai lokacinda take tattaunawa da Amurka.

A wani bangare a maganars Aragchi ya bayyana cewa baya ganin Iran zata farfado da tattaunawa da kasar Amurka nan kusa.

Ya ce: Idan har zamu sake shiga tattaunawa da Amurka sai mun tabbatar da cewa Amurka ba zata kuma kai mana hare-hare a dai-dai lokacinda muke tattaunawa ba.

Ya kara da cewa, tare da wannan tunanin muna ganin sake zama da Amurka kan teburin tattauna ba nan kusa ba. Daga karshe ya ce: a duk sanda muka ga dama ta samu, bama rufe kofar tattaunawa da kowa .

Da aka tamabaye shi dangane da shirin makamashin Nukliya na kasar bayan bom da aka jefa masu. Ministan ya ce: Ai ba’a kauda shirin nukliya da bom. Ko babu shi kwata-kwata zamu sake gina wani daga farko. Sannan idan sun baci ne muna iya sake gyaransu sai mu ci gaba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments