Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Iragchi ya bayyana cewa yana ganin HKI ba zata mutunta yarjeniyar tsagaita wuta da ta cimma da kungiyar Hamas, yace bai amince da alkawalinHKI haka da kasashen yanna.
Yace sune suka zama masu lamuni a tsagaita budewa junawuta a kasar Lebanon tsakanin Hizbullah da kuma HKI, amma manufarsu a tsagaita wuta ne kawai sai suka kyale HKI tana ci gaba kai hare- hare a kan kasar Lebanon ba tare da sun yimagana ba.
Y a ce HKI ta ci gaba da keta hurumin kasar Lebanon tun watan Nuwamban shekara ta 2024 har zuwa yanzu. Tana ci gaba da kashe mutanen kudancin kasar Lebanon, sun kuma hana mutanen yankin su sake gina wurarensu da suka lalace.
Jaridar na Daily Mail ta kasar Burtaniya ta Aragchi yana fadar haka a wata hira ta musamman da yayi da wata tashar Talabijin a nan Tehran.
Sannan ya kara da cewa yana ganin kasashen yamma musamman Amurka a wannan karon ma ba zasu taba cika alkawulan da suka dauka a yarjeniyar sharm sheikh saboda sun saba da yaudara da kuma rashin ciki alkawali.