Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce kasar Iran ta yi maraba a tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo karshen kisan kiyashi

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce kasar Iran ta yi maraba a tsagaita wuta a Gaza da kuma kawo karshen kisan kiyashi wa Falasdinawa, amma ya kara da cewa HKI ba abar amincewa bace, don haka tana iya yaudara da kuma kawo karshen tsagaaita budewa junan wutar gaba daya. Abu ne da saba yi don haka Falasdinawa su yi hattara.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a jiya Asabar ya kuma kara da cewa, Iran tana maraba da dukkan abinda zai kai ga kawo karshen kisan kiyashi a gaza, wanda ya dau shekaru 2 ana yi.

Ministan ya jawo hankalin Hamas da sauran Falasdina kan amincewa da duk abin HKI ta fada, don mayaudara ne kuma basu da cika alkawali. Sun sha sabawa alkawula da aka kulla da su a duk lokacinda suka ga dama.

Yace akwai yiyuwar HKI ko kuma Amurka su sauya ra’ayinsu a ko da yauce, su kuma kawo karshen wannan yarjeniyar a sake komawa yaki, don dabi’arsu ne kuma halinsu ne basa da alkawali.

Ya Palasdinawa sun amince da mataki na farko ne na yarjeniyar, don haka akwai hanya mai wuya a gaba dangane da abinda ya rage na yarjeniyar, wanda za’a ci gaba da tattauna su a nan gaba.

Dangane da sakon shugaban Putin daga HKI, Aragchi ya bayyana cewa, a duk tsawon rigimar JMI ta HKI ita ce ta tsokana, kuma ita farwa kasar da yaki. Don haka Iran a shirye take, kuma tana kara shiri don fuskantar HKI a ko yau. Tun yahudawan baa bar amincewa bace bas u da alkawali.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments