Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ta ce za ta mayar da martani akan hare-haren HKI.
Ofishin siyasa na kungiyar ta Ansarullah ya ce, suna cikin shirin mayar da martani cikin sauri, kuma gwargwagon girman hari za su mayar da martani.
Bugu da kari sanarwar ta ce, harin wuce gona da iri da HKI ta kai, ba zai hana al’ummar Yemen cigaba da taimakon Gaza da al’ummarta da gwagwarmaya ba.
Gwamnatin Sanaa ta sanar da cewa martanin da za ta mayar ba zai dauki lokaci mai tsawo ba.
A jiya Alhamis ne dai HKI ta kai hare-hare akan birnin Sanaa da kuma Hudaidah akan cibiyoyin fararen hula da su ka hada filin jirgin sama da kuma tashar jirgin ruwa.