Ansarullah Ta Yi Allah Wadai Da Sabunta Takunkumin MDD Kan Yemen

Kungiyar Ansarullah a Yemen ta yi Allah wadai da sabunta takunkumin Majalisar Dinkin Duniya Kan kasar tare da dake tabbatar da goyon bayanta ga Falasdinu.

Kungiyar Ansarullah a Yemen ta yi Allah wadai da sabunta takunkumin Majalisar Dinkin Duniya Kan kasar tare da dake tabbatar da goyon bayanta ga Falasdinu.

Kungiyar ta yi tir da matakin da Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Dauka Na sabunta takunkumin Kan Yemen na wata Shekara, ta kuma yi Allah Wadai da son zuciyar kasashen Yamma.

A cikin wani sako a shafin X, Mohammed al-Farah, wani babban jami’i a ofishin siyasa na Ansarullah, ya jaddada kudurin Sana’a na mayar da martani ga duk wanda ya yi yunkurin kai hari ga muradun al’ummar Yemen.

Ya kara da cewa ‘yan Yemen ba za su yi wata-wata ba don kare hakkokinsu, addininsu, da mutuncin kasa, ta kowace hanya da ta dace.

Al-Farah ya kuma kira shawarar da Majalisar Dinkin Duniya ta yanke da “mafi muni a karo na biyu,” yana mai kokawa da cewa hukumar ta yi biris da kisan kiyashin Falasdinawa a Gaza yayin da take goyon bayan gwamnatin Isra’ila a laifukan da take aikatawa da kuma yin watsi da da cin zarafin da take yi wa Yemen.

Babban jami’in ya bayyana Majalisar a matsayin wani dandali da ke biyan muradun Yamma da kuma kare muradun Amurka.

A wani bangare na jawabinsa, ya yaba wa Rasha da China saboda kin sabunta takunkumi kan Yemen, da kuma fahimtar hadarin manufofin Amurka wadda ke amfani da takunkumi ga kasashe masu iko.

Al-Farah ya kuma soki kasashen yamma da Amurka saboda goyon bayansu na soja, kudi, da siyasa ga Isra’ila, yana mai jayayya cewa takunkumin da aka sabunta wa Yemen don biyan bukatun ‘yan Sahayona ne da kuma hukunta al’ummar Yemen saboda juriyarsu, da kuma goyan bayan Gaza.”

Ya kuma sake jaddada goyon bayan Yemen ga Gaza da al’ummomin da ake zalunta a duk fadin yankin, tare da shan alwashin ci gaba da kalubalantar zalincin kasashen Yammacin duniya da Amurka a kan kasashe da al’ummomin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments