Ansarullah: Dakarunsu A Shirye Suke Don Tunkarar Duk Wata Barazana Daga Isra’ila

Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar Ansarullah Abdul-malik al-houthi yayi gargadin cewa yankin yana gab da fuskantar gagarumin rikici da isra’ila da kasashen yamma a

Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar Ansarullah Abdul-malik al-houthi yayi gargadin cewa yankin yana gab da fuskantar gagarumin rikici da isra’ila da kasashen yamma a yanki, don haka yasha alwashin cewa  tsayin dakar dakarun kasar yafi karfi fiye da  baya kuma a shirye take ta kalubalanci duk wanda yayi mata shisshigi a nan gaba.

Wadannan kalaman suna nuna irin yadda ake samun karuwar fadace-fadace a yammacin asiya yayinda kungiyoyin dake goyon bayan yan gwagwarmayar daga yaman da labanon  ke ciin shirin ko ta kwana na yaki da isra’ila da kawayenta na kasashen turai, haka kuma jawabin ya jaddda irin dabarun yaki da kungiyoyin yan gwagwarmaya da isra’ila suka bi  bayan yakin gaza da kuma sabunta kokarin sojojin Amurka a yankin

A bayanin da yayi ta gidan talabijin din kasar game da makon shahidai na kasar, Abdulmalik al hothi ya bayyana matsayin kasar yamen na tunkarar duk wata barazana daga wadanda ya kira da makiya kasashen musulmi, yace duk da kalubalen da suka fuskanta a baya amma kungiyar ansarullah ta kara karfi fiye da baya, kuma yayi barazanar yiyuwa fadawa cikin wani yaki kwanan nan, inda ya zargi isra’ila da ci gaba da kai hare hare agaza bayan yarjejeniyar dakatar da bude wuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments