Shugaban Kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sheikh Abdulmalik al-Husy ya bayyana cewa; Amurka da Da “yan mamaya ‘yan sahayoniya ne tushen duk wani sharri da rashin tsaro a duniya.
Sayyid Abdulmalik wanda ya gabatar da jawabi dazu da marece, ya ce Amurka da ‘yan sahayoniyar sun tabbatarwa da duniya cewa su ne barazana ga tsaro da suka mayar da yaki sana’a suna wawason duniyar al’ummu tun daga Falasdinu zuwa wasu yankuna na duniya.
Sayyid Abdulmalik al-Husy ya kuma ce; Manufar ‘yan sahayonia ta sauya yankin gabas ta tsakiya shi ne ummul-haba’isin dukkanin yake-yaken da ake yi a wannan yankin.
Haka nan kuma shugaban kungiyar ta Ansarullah ya ce, bayan ga rashin girmama dokokin kasa da kasa da Amurka da ‘yan sahayoniya suke yi, sun kuma mayar da hankali wajen yi wa al’ummu kisan kiyashi da rusa ci gaban al’ummu, har kuma suna yi alfahari da hakan.
Da yake Magana akan Saudiyya kuwa, shugaban na kungiyar “Ansarullah” ya zarge ta da zama mai bin ra’ayin kasashen turai. Ya kuma yi Ishara da harin bayan nan akan kasar Yemen yana mai cewa, kokadan Saudiyyar ba abinda ya shafe ta da girmama rayukan mutane da kare mutuncinsu don haka suke ci gaba da killace kasar.
Sayyid Abdulmalik al-Husy ya bayyana yadda killace kasar da aka yin a cewa ya hana al’ummar kasar cin moriyar albarku da duniyar da Allah ya huwace musu.