Angola Zata Shiga Shirin ‘Yankunan Kasuwanci’ Na Kungiyar SADC

Kasar Angola ta bada sanarwan cewa, zata shiga shirin kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC na yankunan kasuwanci, wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen

Kasar Angola ta bada sanarwan cewa, zata shiga shirin kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC na yankunan kasuwanci, wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen yankin .

Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa shigar Angola cikin tsarin yankunan kasuwanci, SADC kuma a matsayin mamba na 14 a wannan tsarin zai dauke kudin fito tsakanin kasashen 13 da Angolar. Wannan har’ila yau zai kara fadin kasuwar kasashen kungiyar ta SADC.

Labarin ya kara da cewa bayan tattaunawa mai tsawo daga karshe Angola ta sami amincewar mafi yawan kasashen kungiyar ta SADC mai mambobi 16.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments