A dai-dai lokacinda ake bukukuwan ranar kare hakkin bil’adama ta duniya, an zirgi sojojin Najeriya ta take hakkin fararen hula a kasar tun bayan bullar kungiyar yan ta’adda ta book Haram a kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a wani taron da hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa wato ‘ the National Human Rights Commission (NHC) ta shirya a Abuja. Babban birnin kasar, an zargin sojojin kasa da kashe fararen hula kimani 10,000 da kuma peyadi ga mata a wasu lokuta a cikin sansanonin yan gudun hijira a arewacin kasar.
Babban sakataren hukumar NHC Dr Tony Ojukwu ya zargi kamfanin dillancin labaran reuters na kasar Burtaniya da rashin bada hadin kai don gano gaskiyan zargin da akewa jami’an tsaro a Najeriya dangane da take hakkin bil’adama da kuma kashe fararen hula a lokacinda suke aikinsu.