Ana Zaman Dar-dar A Kasar Zimbabwe Saboda Shirin Zanga-zangar Tsofaffin Sojaji

Jami’an tsaro sun bazama akan titunan manyan garuruwan kasar Zimbabwe domin dakile zanga-zangar da ake shirin yi domin yin kira ga shugaban kasa Emmerson Mnangagwa

Jami’an tsaro sun bazama akan titunan manyan garuruwan kasar Zimbabwe domin dakile zanga-zangar da ake shirin yi domin yin kira ga shugaban kasa Emmerson Mnangagwa ya yi murabus.

Tsofaffon sojoji da mayakan da su ka samarwa kasar ‘yanci ne dai suka yi kiran a yi zanga-zangar, saboda kin amincewa da shirin shugaban kasar na tsawaita wa’adin mulkinsa.

A cikin watan Janairu na wannan shekarar ne dai jam’iyyar ZANU-Party, mai mulki a kasar ta sanar  da cewa tana son Mnangagwa ya ci gaba da rike mukamin shugaban kasar har zuwa 2023.

Mnangagwa dai ya hau karagar mulkin kasar ta Zimbabwe ne tun a 2017,bayan sauke Robert Mugabe daga kan karagar mulki cikin ruwan sanyi.

Shugaban mayakan nemawa kasar ‘yanci Blessed Geza ya zargi shugaban kasar da cin hanci da rashawa da kuma yi wa kujerar mulki rikon danko.

Shugaban kasar ta Zimbabwe dai ya sha bayyana cewa, ba ya da nufin tsawaita lokacin shugabancinsa.

Kundin tsarin mulkin Zimbabwe wanda aka rubuta a 2013 ya kayyade wa’adin shugabancin kasar na shekaru biyar sau biyu.

Share

5 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments